Deepika Padukone: Hukumomi sun yi wa tauraruwar tambayoyi kan mutuwar Sushant Singh Rajput
Fitacciyar jarumar fina-finan India na Bollywood Deepika Padukone na shan tambayoyi a hannun hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi sakamakon wani bincike da ake yi mata wanda yake da alaƙa da mutuwar jarumi Sushant Singh Rajput.
Padukone na daga cikin mutum shida da aka yi sammacin su - wasu jaruman biyu su ma za su sha tambayoyi ranar Asabar.
An kama budurwar Rajput, Rhea Chakraborty, a farkon watan nan bisa zargin sai wa marigayin ƙwayoyi - zargin da ta musanta.
Kafafen yaɗa labarai a India sun shafe watanni suna rahotanni a kai.
'Yan fim Sara Ali Khan da Shraddha Kapoor na daga cikin mutanen da za a yi wa tambayoyi ranar Asabar, a cewar wasu rahotanni. Ita kuma jaruma Rakul Preet Singh an yi mata tambayoyi ranar Juma'a.
An tsinci gawar Rajput, mai shekara 34 a gidansa da ke Mumbai ranar 14 ga watan Yuni. Ƴan sanda a lokacin sun ce shi ne ya kashe kansa.
Amma ƴan uwansa sun shigar da Chakraborty ƙara wajen ƴan sanda, inda suke zarginta a hannu a lamarin da ma wasu laifuffukan - zarge-zargen da duka ta musanta.
A yanzu dai hukumomi uku ne suke gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai rashin samun bayani daga hukumomi ya sa ana yawan samun jita-jita kan ainihin abin da ya faru.
Ya batun yake?
Hukumar kula da miyagun ƙwayoyi NCB na yin bincike kan abu biyu - binciken farko shi ne kan Rhea Chakraborty, da ɗan uwanta da kuma tsohon mai kula da gidan Rajput.
Dukansu uku an kama su ne bisa zarginsu da shiryawa da kuma ba da gudummawa wajen shan tabar wiwin da jarumin ya sha. Sun musanta zargin aikata laifi.
Bincike na biyu wanda ya biyo na farkon shi ne kan zargin yawan yin amfani da miyagun ƙwayoyi a Bollywood, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar.
Hukumomi suna ta ɓoye bayanan binciken lamarin da ke ƙara janyo jita-jita.
A lokacin mutuwar Rajput, hankali ya lkarkata ne kan Chakraborty wadda ta tsinci kanta cikin zarge-zarge da jita-jita.
A wani ɓangare na binciken da suke yi, jami'an hukumar NCB sun ce suna yin bincike kan wasu saƙonni da aka tura ta kafar sadarwar Whatsapp inda ake zargin a cikinsu Chakraborty take yin magana kan miyagun ƙwayoyi.
Yayin da aka haramta tabar wiwi a India, wani nau'inta da ake kira bhang - doka ta amince da shi kuma ana amfani da shi.
Me ya hada Deepika Padukone da shi?
Har yanzu ba a san komai ba kan haka.
Jami'an da ke bincike kan miyagun ƙwayoyi sun ce suna tambayoyi ne kan saƙonnin Whatsapp tsakanin Padukone da kuma masu kula da ayyukanta, a cewar kafafaen yaɗa labarai na ƙasar. Amma har yanzu ba a da masania kan bayanan da ke ƙunshe cikin saƙonnin.
Wasu sun ce ana tuhumarta ne saboda a watan Janairu ta kai ziyara wata jami'a inda wasu ɗalibai masu alaƙa da jam'iyyar BJP ta Firaminista Narendra Modi ke kai hari kan wata tawagar ɗalibai.
Masu goyon bayan BJP sun zargi jarumar da jan hankalin jama'a har a shafin Tuwita kan sabon fim ɗinta, sun dai buƙaci mutane su yi nesa-nesa da fim ɗin.
A cewar jaridar Times of India, jami'ai na iƙirarin cewa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi da suka yi wa tambayoyi sun ambaci sunayen wasu 'yan fim mata.
Ma'abota shafukan sada zumunta suma suna tambaya me ya sa yin tambayoyin da hukumomi ke yi ya shafi 'yan fim mata - ba wai maza ba.
Amma lamarin da ya faro daga bincike kan mutuwar jarumin ya zama wani abin na daban cikin 'yan makonni.
Kuma yanzu kafafen yaɗa labarai na ci gaba da mayar da hankali kan labarin.
Me ake ta cewa?
Yawan sa labarin a talbijin ya sa mutane da dama na ayar tambaya kan lamarin.
Cikin watanni, kafafen yaɗa labarai ba su ragawa mutanen da ke da kusanci da Rajput ba - likitansa da abokansa da ƴan uwansa da abokan aikinsa da ma tsohon mai yi masa girke-girke.
Sannan rashin samun bayani daga jami'ai, kafafen yaɗa labarai suna shafe sa'oi suna sharhi kan ƴan bayanan da suka samu game da batun.
A ƙoƙarin nuna cewa Chakraborty na da hannu a kudaden Rajput, wani gidan talabijin ya yi ƙoƙarin fassara sakonnin da ake zargi daga wayarta.
Wannan lamarin dai ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Wasu da yawa na magana kan ko tsawon lokacin da aka shafe ana magana kan lamarin ya ɗauke hankalin mutane daga batutuwan da suka shafi mutane a India a wannan lokacin - batun cutar korona inda ƙasar ce ta biyu a yawan masu fama da cutar da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma taɓarɓarewar dangantaka da China.
Comments
Post a Comment